in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta ce za a shirya taron kolin Afirka don bibiyar aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar Sudan ta kudu
2019-03-28 10:01:40 cri

A ranar Laraba kasar Sudan ta sanar da cewa, za'a shirya taron kolin Afirka da nufin bibiyar yadda ake aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar Sudan ta kudu wacce aka sanyawa hannu a watan Satumbar bara.

"Za a gudanar da taron kolin na Afrika ne domin yin dubi game da abubuwan da aka cimma nasara kansu cikin wa'adin da aka kebe na wucin gadi, wanda ake sa ran zai kammala a watan Mayu mai zuwa, da irin kokarin da ake yi na tabbatar da nasarar da aka sanya a gaba." ministan harkokin wajen kasar Sudan Al-Dirdiri Mohamed Ahmed ne bayyana hakan ga 'yan jaridu.

Sai dai bai fayyace takamamman inda za'a gudanar da taron kolin ba.

A ranar 13 ga watan Satumbar shekarar da ta gabata ne, bangarorin dake yaki da juna a Sudan ta kudu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha a gaban shugabannin kungiyar raya shiyyar gabashin Afrika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China