in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta yi watsi da kalaman Birtaniya da Norway da Amurka game da zanga zangar kasar
2019-01-10 10:04:11 cri

A jiya Laraba gwamnatin kasar Sudan ta sanar da cewa, ta yi watsi da kalaman da gamayyar kasashen dake kiran kan su Troika wato Birtaniya, Norway da Amurka suka yi, tare da kasar Canada game da zanga zangar da ta barke kwanan nan a kasar ta Sudan.

"Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta yi watsi da kuma yin Allah wadai da kalaman rashin adalci, wadanda sun ci karo da hakikanin halin da ake ciki, wanda aka fitar da su a ranar Talata daga ofisoshin jakadancin kasashen na Troika da Canada, game zanga zangar dake faruwa a wasu sassan kasar, kuma hukumomin da abin ya shafa suna daukar matakan da suka dace." in ji ma'aikatar harkokin wajen ta Sudan.

Ma'aikatar ta kuma yi watsi da barazanar da Troika suka nuna cikin sanarwar, inda ta jaddada matsayin Sudan a matsayin yantaciyyar kasa mai ikon kanta, da kare ikon mulkin kasarta tare kuma da yin watsi da duk wani yunkuri na yin shisshigi ga duk wasu batutuwa da suka shafi harkokin cikin gidan kasar.

A ranar Talata, Troika da Canada suka fidda wata sanarwa, inda suke bayyana matukar rashin jin dadinsu game da irin matakin da gwamnatin Sudan ta dauka na martani kan masu zanga zanga a kasar Sudan, da kuma garkame masu fafutukar tabbatar da siyasa a kasar da masu zanga zanga ba tare da yi musu shari'a ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China