in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban majalisar dokokin Kamaru ya bukaci a kara fahimtar rikicin yanki mai magana da Turanci
2019-04-11 10:33:11 cri

Shugaban majalisar dokokin jamhuriyar Kamaru Cavaye Yeguie Djibril ya bukaci al'ummar kasa da kasa da su kara kyakkyawar fahimtar ainihin tashin hankalin da ake fama da shi a yankunan biyu masu magana da yaren Turanci a kasar ta yammacin Afrika, domin kaucewa nuna son kai da fifiko ga kungiyoyin masu dauke da makamai.

"Yanayin tsaro shi ne muhimmin batu wanda ya mamaye kusan dukkan batutuwan da suka shafi kasarmu, musamman a yankunan arewa masu yammaci da kudu maso yammacin kasar," in ji Djibril wanda ya bayyana hakan a lokacin zaman majalisar dokokin kasar.

"Akwai abubuwa masu tarin yawa aka aiwatar da su, amma matakan da aka dauka na baya bayan nan sun nuna cewa za mu samu nasara a nan gaba."

"Muna fatan za'a yi mana kyakkyawar fahimta, da nuna adalci da goya mana baya bisa ga irin huldar da muke da ita tsakanin kasa da kasa da kuma gamayyar kasashen duniya wajen tunkarar rikicin kasar,"in ji shi.

Djibril ya yi Allah wadai da halayyar wasu kungiyoyin kasa da kasa, bisa abin da ya kira nuna keta da rufe idonsu da gangan kan tashin hankalin da kungiyoyi masu dauke da makamai ke yi a sassan kasar, inda kuma suke dora alhaki kan gwamnati.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China