in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan makarantar da aka sace a kamaru sun kubuta
2018-11-09 10:28:40 cri

Daukacin 'yan makarantar sakandare su 79 da direban su, wadanda wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da su daga garin Bamenda na yankin arewa maso yammacin kasar Kamaru sun kubuta, har ma wasu rahotanni sun tabbatar da cewa, sun koma ga iyalan su.

Da yake tabbatar da hakan, shugaban makarantar ta Presbyterian, rabaran Samuel Fonki, ya ce al'ummar yankin sun cika da farin ciki, sakamakon sako yaran da masu garkuwa da su suka yi. To sai dai kuma Mr. Fonki ya ce makarantar za ta ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa wani lokaci a nan gaba.

Shi ma ministan ilimin kasar ta Kamaru Issa Tchiroma, ya ce an saki 'yan makarantar ne a ranar Laraba, bayan garkuwa da su tsawon kwanaki hudu. Gwamnatin kasar dai ta zargi 'yan awaren kasar dake magana da Turancin Ingilishi da sace yaran, ko da yake 'yan awaren sun musanta wannan zargi, suna masu cewa gwamnatin kasar ce ta kitsa sashe yaran, domin shafawa fafutukar da suke yi ta samun 'yancin kai kashin kaji.

A daya hannun kuma, rundunar sojojin kasar ta Kamaru, ta ce kawo yanzu shugaban makarantar, da wani malami guda, na tsare a hannun wadanda suka yi garkuwa da yaran.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China