in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yanayin bukatar agaji ya tsananta a yankin dake magana da Turanci a Kamaru
2019-01-26 15:07:07 cri

Kakakin MDD ya yi gargadi a ranar Juma'a cewa, yanayin kai agaji ga al'umma yana ci gaba da tabarbarewa a jamhuriyar kasar Kamaru a yayin da ake kara fuskantar tashe tashen hankula a shiyyoyin arewa maso yamma da kudu maso yammacin yankunan dake magana da yaren Turanci.

Ofishin dake kula da ayyukan tallafin jin kai na MDD ya yi gargadin cewa, yanayin bukatar tallafin na ci gaba da karuwa kuma akwai yiwuwar al'amarin zai ci gaba yayin da yankuna 8 daga cikin yankunan kasar 10 na kasar na fuskantar barazanar tashe-tashen hankulia, musamman yankunan arewa maso yamma da kudu maso yammacin kasar, Farhan Haq, mataimakin kakakin babban sakataren MDD shi ne ya bayyana hakan.

Ya ce, mutane miliyan 4.3 ne ke cikin matsananciyar bukatar a kai musu dauki, inda aka samu karin kashi 31 bisa 100 na bukatar daga shekarar 2018.

Wani shirin samar da agaji na hadin gwiwa na shekarar 2019 wanda aka gabatar da shi a Geneva, yana neman kudi kimanin dalar Amurka miliyan 299 domin tallafawa mutane miliyan 2.3, Haq ya bayyana hakan ne ga 'yan jaridu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China