in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamaru: An yi garkuwa da wani tsohon jami'i a yanki mai magana da Turanci
2019-03-21 10:27:24 cri

Hukumomin jamhuriyar Kamaru sun ce, an yi garkuwa da wani tsohon jami'in gwamnatin kasar da safiyar ranar Laraba a wani yanki mai magana da yaren Turanci dake shiyyar arewa maso yammacin kasar mai fama da tashe tashen hankula.

Emmanuel Ngafeson Bantar, wanda ya taba rike mukamin sakatare a ma'aikatar shari'a ta kasar mai kula da sha'anin gidajen yari, an yi garkuwa da shi ne a Bamenda, birnin mafi girma a yankin mai magana da yaren Turanci a Kamaru, yankin dake fama da yaki tsakanin dakarun gwamnati da mayakan 'yan awaren Ambazoniya.

"Yana gida a tare da iyalinsa, a sai kawai 'yan bindiga suka shiga gidan kana suka umarce shi ya shiga motarsa. Daga nan sai suka awon gaba da shi zuwa wani wajen da ba'a san ko ina ne ba." Wani jami'in yankin ne da ya bukaci a sakaye sunansa ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

"Gwamnati tana daukar dukkan matakan da suka dace don tabbatar da an sako shi," in ji jami'in.

Wasu daga cikin iyalinsa da Xinhua ta zanta da su sun ce, masu garkuwar suna dauke da muggan makamai, kuma ba su nemi kudin fansa ba.

Bantar shi ne jami'in gwamnati na farko wanda ya yi aiki dake da kusanci da shugaban kasar Paul Biya wanda aka yi garkuwa da shi a yankin arewa maso yammacin kasar, daya daga cikin yankuna biyu da suka fi fama da rikici masu magana da yaren Turanci, tun bayan da tashin hankalin kasar ya barke a watan Nuwambar shekarar 2017.

Haka zalika da safiyar ranar Larabar, wasu 'yan wasan kwallon kafa na jami'ar Buea ta kasar su 15, an yi garkuwa da su a yankin na Buea, babban birnin yankin mai magana da yaren Turanci dake shiyyar kudu maso yammain kasar, kamar yadda hukumomin jami'ar suka bayyana.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China