in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci 'yan kasuwar Zambiya su yi amfani da sashen Sin domin shiga kasuwar kasar
2019-04-11 10:20:41 cri

Hukumar zuba jarin kasar Zambiya ta bukaci 'yan kasuwar kasarta dake fitar da kayayyaki zuwa ketare da su yi kyakkyawan amfani da sashen kasar Sin da aka bude a hukumar wato "China Desk" domin samun damar shiga kasuwannin kasar Sin.

Hukumar raya ci gaban Zambiya ta sanar cewa, an bude sashen ne domin samar da muhimman shawarwari da kuma ka'idojin da suka shafi zuba jari ga Sinawa masu zuba jari da samun kyakkyawar makoma na wasu muhimman damammaki ga masu sha'awar zuba jari da kuma masu son yin hadin gwiwar cinikayya tsakanin 'yan kasuwar kasashen biyu.

Cikin wata sanarwa, hukumar zuba jarin ta ce ta kafa wannan sashe ne tare da hadin gwiwar cibiyar ciniki ta kasa da kasa ta hanyar hadin gwiwar shirin zuba jari da raya ci gaba na Afrika wato (PIGA) domin bunkasa harkokin cinikayya da hadin gwiwar 'yan kasuwar kasashen Zambiya da Sin.

Kafa wannan sashe yana kara tabbatar da yadda ake kara samun bunkasuwa da kuma dora muhimmanci ga kasar Sin a matsayin abokiyar huldar kasuwanci da zuba jari ta Zambiya, in ji hukumar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China