in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya bukaci a zuba kudade wajen tunkarar matsalar sauyin yanayi a Afrika
2018-10-18 10:05:24 cri

Bankin duniya ya bukaci a kara zuba kudade wajen samar da fasahohin zamani da za'a yi amfani da su don tunkarar matsalolin sauyin yanayi, musamman a kasashen Afrika.

Mataimakin shugaban bankin duniya mai kula da Afrika Hafez Ghanem, wanda a halin yanzu yake kasar Zambiya domin ziyarar aikin kwanaki uku, ya ce yana da matukar muhimmanci a kara samar da kudade domin samar da fasahohin zamani don ayyukan sauyin yanayi a Afrika saboda illolin da matsalar sauyin yanayin ke haifarwa.

Da yake jawabi a lokacin ganawa da ministar kudin kasar Margaret Mwanakatwe, jami'in bankin duniyar ya ce, zuba kudade domin samar da fasahohin zamani don tunkarar sauyin yanayi, abu ne mai matukar muhimmanci saboda irin barazanar da matsalar ke yiwa fannin aikin gona da samar da abinci a nahiyar Afrika.

Ya ce, bankin duniyar yana taimakawa kasar Zambiya wajen aiwatar da ayyuka masu yawa ta hanyar samar da rancen dala biliyan 1.2 karkashin shirin nan na ba da tallafin ci gaba na kasa da kasa wato IDA.

Ya ce, shirin na IDA, wanda aka fara gudanar da shi tun shekara guda da rabi da ta gabata yana mayar da hankali ne wajen taimakawa rayuwar mata da 'yan mata, da inganta fannin kiwon lafiya da kuma samar da hasken lantarki.

Bugu da kari, jami'in ya ce, za'a gudanar da taron bibiyar shirin na IDA na tsakiyar zango a birnin Livingstone na kudancin Zambiya a wata mai zuwa da nufin duba irin nasarorin da aka samu karkashin shirin na IDA ya zuwa yanzu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China