in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zambia ta kaddamar da tashar talabijin ta zamani da Sin ta samar a kauyuka 500
2018-06-26 10:55:56 cri

A jiya Litinin kasar Zambiya ta kaddamar da aikin tashar talabijin ta zamani wanda kasar Sin ta gudanar inda za ta baiwa mutanen dake zaune a kauyuka 500 damar yin amfani da tashar talabijin mai tauraron dan adam a kasar ta kudancin Afrika.

Aikin, na daga cikin ayyukan samar da tashoshin talabijin na zamani a kauyukan Afrika kimanin dubu 10, wanda kamfanin StarTimes na kasar Sin ke daukar nauyi, kuma ana sa ran kammala aikin a wannan kasa kafin karshen shekarar nan ta 2018.

Shugaban kasar Zambian Edgar Lungu, da wasu jami'an ofishin jakadancin kasar Sin ne suka halarci bikin wanda aka gudanar a gundumar Vubwi dake gabashin kasar Zambia.

Jami'in sashen ciniki da tattalin arziki na ofishin jakadancin kasar Sin Ouyang Daobing ya ce, kaddamar da aikin samar da tashar talabijin ta zamani wanda aka gudanar, wani muhimmin ci gaba ne wajen raya al'adu da yin mu'amala tsakanin mutum da mutum na jama'ar kasashen Sin da Zambia, kuma daya ne daga cikin manyan nasarorin da aka cimma karkashin yarjejeniyoyi 10 da aka cimma a taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC a shekarar 2015.

Ya ce, kasar Zambia tana daga cikin sahun farko na kasashen da aka aiwatar da ayyukan.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China