in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya da Zambiya za su yi hadin gwiwar bunkasa tattalin arziki da samar da tsaro
2018-06-18 15:48:56 cri

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta da takwaransa na Zambiya Edgar Lungu sun cimma matsayar yin hadin gwiwa don bunkasa tattalin arziki da tabbatar da tsaro a tsakanin kasashen biyu.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugabannin biyu suka fitar a Nairobi, bayan taron tattaunawa da suka gudanar sun cimma matsayar karfafa hadin gwiwa a bangarori da dama da suka hada da fannin yawon bude ido, sufuri, cinikayya, zuba jari, sararin samaniya da kuma tsaron shiyyoyin kasashen biyu.

Daga cikin yarjejeniyar da suka cimma game da hadin gwiwar kasashen a fannin yawon bude ido, kasar Kenya wadda ta samu kwarewa mai yawa a fannin, za ta horas da daliban kasar Zambiya kimanin 50 a fitacciyar kwalejin nan ta Kenya Utalii. Kuma za'a fara aikin ba da horon ne nan ba da jimawa ba da zarar an kammala dukkan shirye shiryen da suka dace.

Dama dai kasashen biyu sun jima suna cin moriyar juna karkashin hadin gwiwarsu a fannonin aikin gona, yawon shakatawa, ilmi da fasahar sadarwa ta zamani.

Shugaban kasar Zambia, wanda a halin yanzu yake wata ziyara ta kashin kansa a Kenya, ya ziyarci wata kwaleji dake garin Kilifi a gabar tekun kasar, ya yaba da irin ci gaban da Kenya ta samu a bangaren yawon bude ido.

A cewar fadar shugaban kasar ta Kenya, kasashen biyu sun jima da kulla yarjejeniyoyi a fannonin kimiyya, fasaha, da kuma kirkire kirkire.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China