in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shelter Afrique zai hada kai da Sin don magance matsalar gidaje a Afirka
2019-04-11 09:28:34 cri

Kamfanin nan mai suna "Shelter Afrique" dake samar da kudaden gina gidajen kwana a Afirka, zai duba yiwuwar hada kai da kasar Sin, don magance matsalar gidajen da ake fuskanta a Afirka.

Shugaban kamfanin Andrew Chimphondah ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Nairobin Kenya cewa, gwamnatocin kasashen Afirka 44 na da kaso 78 cikin 100 na jarin kamfanin wato mataki na farko, yayin da bankin raya Afirka da hukumar inshora ta Afirka ke da kaso 22 cikin 100 wadda shi ne mataki na biyu na hannayen jarin.

Chimphondah wanda ya bayyana haka a gefen taron shekara-shekara na dandalin zuba jarin kadarori na gabashin Afirka karo na 6, ya ce yanzu haka, an bullo da sabon mataki na uku na hannayen jari, wanda kamfanin ke fatan sayarwa hukumomin kudi na kasar Sin, matakain da zai ba su damar sayen hannayen jarin kamfanin na "Shelter Afrique", ta yadda za su taimaka wajen samar da gidaje masu saukin kudi a Afirka.

Jami'in ya kuma lura cewa, jarin da Sinawan za su zuba, zai taimaka wajen samar da rukunin gidaje a kalla 1,000 a sassan nahiyar, a wani mataki na cike gibin gidajen da ake fuskanta. Ya ce, yanzu haka, akwai gibin rukunin gidaje kimanin miliyan 100 a Afirka, inda manyan kasashen nahiyar kamar Najeriya ke da gibin gidaje kusan miliyan 17, sai Kenya da Afirka ta kudu masu miliyan uku-uku kowanne, yayin da Ghana ke da gibin rukunin gidaje miliyan biyu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China