in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawarar ziri daya da hanya daya tana karfafa alakar Sin da Afirka
2019-03-20 10:16:59 cri

Kwararre game da alakar Sin da kasashen Afirka Cavince Adhere, ya ce taron masu ruwa da tsaki game da shawarar ziri daya da hanya daya dake tafe nan ba da jimawa ba, zai kara karfafa alakar Sin da kasashen nahiyar Afirka.

Cavince Adhere, ya bayyana hakan ne a jiya Talata, yayin zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Nairobin kasar Kenya, a gefen taron karawa juna sani na kwararru, da kafafen watsa labarai, game da ci gaban da aka samu wajen ayyukan shimfida layin dogo na zamani. Ya ce, Sin da Afirka manyan kasuwanni ne a duniya, wadanda kuma suke bukatar juna domin ci gaban su. Adhere ya kuma jinjinawa zabar gabashin Afirka da aka yi, a matsayin wani jigo na aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya. Ya ce Kenya ta amfana matuka daga wannan tsari na shimfida layin dogo da ya hada tashar bakin ruwa ta birnin Mombasa zuwa Nairobi, fadar mulkin kasar, aikin da ya zamo mafi girma a tarihin samar da ababen more rayuwa a kasar.

Taron da aka tsara gudanarwa a kasar Sin, zai samar da dama ga sassan biyu, ta sake nazartar nasarorin da suka cimma kawo yanzu, wajen aiwatar da muhimman ayyuka karkashin inuwar shawarar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China