in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da kasashen Afirka na fatan bunkasa kayayyakin more rayuwa masu inganci
2019-03-19 10:02:58 cri

Daraktan hukumar tabbatar da nagartar ayyuka ta kasar Sin Huang Guoliang, ya ce karkashin shawarar ziri daya da hanya daya, Sin da kasashen nahiyar Afirka, na fatan ingantawa, da samar da ayyukan more rayuwa masu cikakkiyar kariya.

Huang Guoliang, ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a birnin Nairobi na kasar Kenya, yayin taron masu ruwa da tsaki da ya gudana, yana mai cewa, hakan wani mataki ne na inganta ci gaban alakar sassan biyu, duba da cewa, shawarar ziri daya da hanya daya ta shafi Sin da kuma sauran sassa na duniya ne baki daya. Jami'in ya kara da cewa, shawarar za ta fadada damar cin gajiya, da tattaunawa mai zurfi, tare da baiwa juna tallafin da ya dace.

Taron dai na da nufin zakulo dabarun aiwatar da manufofin da aka tsara, ta hanyar magance matsaloli, da kalubalen da ka iya biyo bayan matakan aiwatar da manufofin.

Taron ya samu halartar wakilai daga hukumomin MDD, da na kungiyoyin injiniyoyi, da kungiyar masu kere kere ta kasar Kenya (KAM), da takwararta ta kasar Tanzania da Morocco, da wakilan kamfanonin kasar Sin dake zuba jari a nahiyar Afirka.

Yayin da yake tsokaci, jagoran kungiyar KAM Sachen Gudka, ya ce masu masana'antu na da burin inganta gudanar da hadin gwiwa tsakanin Sin da masu kamfanonin kere kere na kasar Kenya, domin cin gajiyar sassan biyu.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China