in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da gidauniyar gasar 'yan kasuwa ta Jack Ma a Kenya
2019-03-28 11:04:43 cri

A ranar Laraba aka kaddamar da gidauniyar shirya gasar 'yan kasuwa ta ANPI a kasar Kenya wanda babban attijirin nan 'dan kasar Sin mai kamfanin Alibaba Group Jack Ma ya kafa da nufin kyautata dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika.

Sam Gichuru, babban jami'in Nailab, wanda ke kula da gidauniyar ANPI a nahiyar Afrika da shiyyar gabashin Afrika, shi ne ya tabbatar da hakan ga 'yan jaridu a Nairobi cewa, an shirya gasar ne ga 'yan kasuwar Afrika dake kasuwanci a Afrika.

"Matakin zai taimaka wajen bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika saboda hakan ya kara nuna cewa, kasar Sin tana kara kulla alaka da kasashen Afrika, kuma tana mayar da hankali wajen taka muhimmiyar rawa domin cire mutane daga kangin fatara ta hanyar sana'o'in dogaro da kai," in ji Gichuru.

Tuni dai aka kaddamar da manhajar gidauniyar ta ANPI a kasashen Najeriya, Masar, Kenya da Afrika ta kudu.

Gasar 'yan kasuwar ta Afrika wadda gidauniyar Jack Ma ta kafa, kuma a cikin shekaru 10 masu zuwa, ANPI za ta shirya babbar gasa ta dukkan kasashen Afrika, inda za'a tantance mutane 10 da suka samu nasara wadanda za su fafata a gasar cin dala miliyan 1.

Gichuru ya ce, ana sa ran gidauniyar ANPI za ta fara karbar takardun masu nuna sha'awar shiga gasar daga ranar 27 ga watan Maris zuwa 30 ga watan Yuni.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China