in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da EU sun fitar da sanarwar hadin gwiwa kan ganawar shugabannin sassa karo na 21
2019-04-10 09:41:36 cri

Kasar Sin da kungiyar tarayyar Turai, sun nanata kyakkyawar alakar dake tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare, tare da alkawarin martaba tsarin cudanyar kasashen duniya da nuna rashin amincewa da tsarin ba da kariya ga harkokin cinikayya.

Bangarorin biyu sun bayyana hakan ne cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a jiya Talata, bayan ganawa tsakanin firaministan kasar Sin Li Keqiang da shugaban kungiyar tarayyar Turai Donald Tusk da na hukumar gudanarwar kungiyar Jean Claude Junker yayin taron shugabannin Sin da EU karo na 21.

Sassan biyu sun kuma nanata kudirinsu, na martaba dokokin kasa da kasa da muhimman ka'idojin tafiyar da harkokin alakar kasa da kasa, karkashin jagorancin MDD.

A cewar sanarwar, bangarorin biyu za su martaba kudirorin MDD da dokokin kasa da kasa, da ma ginshikan tsarin MDD guda uku, wato zaman lafiya da tsaro da ci gaba kuma kare hakkin bil-Adam.

Haka kuma, kasar Sin da EU suna goyon bayan dokokin cinikayya tsakanin kasashen duniya karkashin jagorancin kungiyar cinikayya ta duniya(WTO), da yaki da cudanyar kasashen duniya da batun ba da kariya ga harkokin cinikayya, da martaba dokokin kungiyar WTO sau da kafa.

Bangarorin biyu, sun kuma goyi bayan kungiyar kasashen G20 ta ci gaba da taka rawa a matsayin dandalin tattauna harkokin tattalin arzikin duniya da alakar harkokin kudi. A halin da ake ciki kuma, sassan biyu, sun nanata kudirinsu na gina alakar tattalin arziki mai salon bude kofa ga kowa, da nuna rashin bambanci, da yin takara cikin adalci, da yin komai a bayyane ta hanyar samun moriyar juna.

A cewar sanarwar, hakan na nuna, kasar Sin da kungiyar EU, za su kara zage damtse wajen lalubo matakan magance tare da amincewa da wasu manyan batutuwa dake hana ruwa gudu a tsakaninsu. Haka kuma sun yi maraba da ci gaban da aka samu a fannin alakar fasahar 5G tsakanin 'yan kasuwan sassan biyu.

Kasar Sin da EU sun kuma yi maraba da sakamakon da aka samu, da kara yin musaya a tattaunawar Sin da EU da bullo da managartan matakai game da fasahar 5G, kamar yadda ke kunshe cikin sanarwar taron hadin gwiwa kan fasahar 5G na shekarar 2015, ciki har da alakar fasahar kere-kere tsakanin 'yan kasuwan al'ummomin da abin ya shafa.

A ranar Litinin ne dai, firaministan na Sin ya isa Brussels. Zangonsa na farko a ziyarar kwanaki biyar da yake yi a Turai. A yammacin jiya ne kuma, ya isa Zagreb a ziyarar aikin da ya fara a kasar Croatia, inda kuma zai halarci taron shugabannin Sin da kasashen gabashin da tsakiyar Turai karo na 8.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China