in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya isa Brussels domin halartar taron shugbannin Sin da na EU
2019-04-09 09:29:26 cri

Firaministan kasar Sin, Li Keqiang, ya isa birnin Brussels a jiya Litinin, domin halartar taron shugbannin kasar Sin da na Tarayyar Turai karon na 21.

Li Keqiang, ya ce kasar Sin da Turai muhimman bangarori ne kuma manyan kasuwanni a duniya, kana muhimman abokan huldar juna.

Ya ce, yana sa ran tattaunawa mai zurfi da bangaren Turai kan alakar dake tsakaninsu da sauran batutuwan dake jan hankalinsu bisa girmamawa da tuntuba da kuma moriyar juna.

Ya kara da cewa, kasar Sin na fatan bangarorin biyu za su cimma matsaya kan dangantaka mai karfi da samun ingantacciyar nasara kan yarjejeniyarsu ta zuba jari, domin kara bunkasa muhimmiyar dangantakar dake tsakaninsu zuwa mataki na gaba, wadda za ta kara fadadawa da zurfafa bangarorinsu na hadin gwiwa.

Ya ce kasar Sin na goyon bayan dunkulewar nahiyar Turai, da ci gaba da hadin kanta, da ma rawar da take takawa kan batutuwan da suka shafi kasa da kasa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China