in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin yana kan hanyarsa ta ziyara a nahiyar Turai
2019-04-08 14:01:24 cri

A yau Litinin firaiministan kasar Sin Li Keqiang ya tashi daga birnin Beijing domin halartar taron tattaunawar shugabannin kasashen Sin da EU karo na 21 a birnin Brussels, da taron manyan shugabannin kasar Sin da kasashen tsakiya da gabashin Turai wato (CEEC) da za a gudanar a kasar Croatia, da kuma ziyarar aiki a wannan kasa.

Daga cikin 'yan tawagar mista Li akwai mai dakinsa Cheng Hong, da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, da He Lifeng, mataimakin shugaban babban kwamitin bada shawara kan harkokin siyasar kasar Sin da kuma shugaban babbar hukumar raya cigaban kasar Sin da gyare-gyarenta.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China