in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira da hadin gwiwa tsakanin manya da matasa
2019-04-09 10:20:12 cri

Shugabar zauren MDD Maria Fernanda Espinosa Garces, ta bayyana muhimmancin dake tattare da hadin gwiwa tsakanin manya da matasa.

Da take jawabi ga taron matasa na majalisar kula da zaman takewa da tattalin arziki ta MDD na shekarar 2019 a jiya, Maria Espinosa, ta ce dole ne manya da matasa su yi aiki tare domin magance kalubalen da ake fuskanta, saboda dukkansu na da nauyin da ya rataya a wuyansu.

Ta ce akwai kalubalen da ya kamata a magance, kamar samar da sabbin guraben ayyukan yi miliyan 344 da ake bukata domin dacewa da karuwar matasa da ake samu.

Ta ce ana daukar matasa a matsayin matsalar dake bukatar magancewa. Sai dai abun da matasan wannan zamani mafiya yawa kuma mafiya ilimi da basira da aka taba samu a duniya za su iya yi, ba shi da iyaka.

Taron na yini 2 mai taken 'wadanda aka karfafawa, ake damawa da su, kuma ba a bambamtawa' wanda aka fara jiya Litinin, zai kunshi taruka daban daban, inda za a tattauna kan batutuwan da suka shafi matasa da kuma yankuna. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China