in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana fatan za a kiyaye zaman lafiya a sararin samaniya
2019-04-03 20:08:22 cri

Yau yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana batun rashin amincewar da aka nuna ga takardar dokar kasashen duniya ta MDD, wadda ke shafar hana takarar a harkokin sararin samaniya cewa, kasar Sin ta yi bakin ciki matuka da wannan sakamako, kuma tana fatan bangarori daban daban da abin ya shafa za su nuna himma domin shiga aikin kwance damara a sararin samaniya, ta yadda za a kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a bangaren.

Jiya ne ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayar da wani labari cewa, kungiyar masanan gwamnatocin kasashen duniya da aka kafa bisa kudurin babban taron MDD ta tattauna kan takardar a Geneva a watan Maris, inda masanan da suka zo daga kasashe 25 kamar su Rasha da kasar Sin da Brazil da sauransu suka tsara takardar, amma Amurka ta hana a amince da ita.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China