in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummar Habasha miliyan 8.86 ne ke bukatar agajin jin kai a 2019
2019-04-09 09:58:55 cri

Ofishin MDD mai kula da ayyukan agajin jin kai (UNOCHA), ya ce al'ummar Habasha miliyan 8.86 ne ke neman agajin jin kai na gaggawa a shekarar 2019.

Sanawar da ofishin ta fitar, ta ce mutanen miliyan 8.86 sun hada da wadanda ke fama da karancin abinci da tamowa da wadanda suka rasa matsugunansu da kuma marasa lafiya.

Sanarwar ta ce, rikice-rikice da iftila'i da barkewar cututtuka ne suka haifar da bukatun agajin.

A watan Maris ne gwamnatin Habasha da abokan huldarta, ciki har da ofishin mai kula da agajin jin kai, suka ce ana bukatar dala biliyan 1.3 na magance bukatun abinci da sauran bukatun gaggawa da ba na abinci ba, na mutane miliyan 8.3 a bana.

Habasha ba ta fuskanci matsalolin dake da alaka da yanayi ba a bara, sai dai an samu karuwar rikice-rikice da suka haifar da rashin matsugunai, wanda ya kusan rubanya adadin 'yan gudun hijirar kasar, lamarin da ya kara yawan agajin jin kai da ake bukata a shekarar 2019. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China