in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin mutanen da suka mutu domin zazzabin Lassa ya kai 93 a Najeriya
2019-03-10 15:28:42 cri

Jiya Asabar hukumar dake yaki da cututtuka masu saurin yaduwa a Najeriya NCDC ta sanar da cewa, daga watan Janairun wannan shekarar, adadin mutanen da suka mutu bayan da suka kamu da cutar zazzabin Lassa a Najeriya ya kai 93.

A wata sanarwar da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Abuja, hukumar ta NCDC ta ce, adadin mutanen da suka mutu bayan da suka kamu da cutar ya kai kashi 22.1 bisa 100 dake cikin daukacin wadanda suka kamu da cutar tun bayan bullarta a kasar cikin watan Janairun da ta gabata.

Annobar zazzabin ta shafi jihohi 21 daga cikin jihohi 36 na kasar tun daga ranar 13 ga watan Janairu, in ji sanarwar. An samu bullar cutar har a wasu yankunan birnin Abuja.

Kawo yanzu, ana tsammanin adadin mutanen da suka kamu da kwayoyin cutar ya kai 1,447 a duk fadin kasar, in ji NCDC.

A ranar 22 ga watan Janairun bana, gwamnatin Najeriya ta ayyana sake barkewar cutar, inda nan take aka kafa cibiyoyin dakile yaduwar cutar ba tare da bara lokaci ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China