in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Sin ya bude masana'antar sarrafa roba a Kenya
2019-04-09 10:05:19 cri

A jiya ne wani kamfanin kasar Sin, ya bude wata masana'antar sarrafa robobi da darajarta ta kai dala miliyan 45 a gabashin kasar Kenya, da nufin rage gurbatar muhalli.

Ana sa ran kamfanin mai suna Weeco, zai rika sarrafa tan dubu 2 na robobin ruwa a kowane wata, inda zai sarrafa su zuwa totuwa da audugar roba.

Baya ga sabuwar masana'antar dake garin kogin Athi, kamfanin Weeco zai kuma bude wata masana'antar a yankin Mombasa dake gabar ruwa.

A jawabinsa, darektan kamfanin Wang Zhangyi, ya ce masana'antar za ta inganta rayuwar mazauna wurin dake tattara da ma samar da robobin ruwa a kowane wata. Yana mai cewa, za a rika fitar da totuwar da masa'antar ke samarwa zuwa babban kamfanin na Weeco dake kasar Sin inda za a rika samar da audugar roba.

Bugu da kari, kamfanin Weeco ya kulla yarjejeniya da kamfanin sarrafa robobi na kasar Kenya (PETCO Kenya), ma'aikatar da aka dora mata alhakin kula da ingancin yadda ake samar da robobin da ake sarrafawa a kasar.

Shi ma da yake jawabi, shugaban PETCO Kenya, John Waithaka, ya yi maraba da wannan yarjejeniya, yana mai cewa, matakin kamfanin Weeco na sarrafa robobin ruwa, ya dace da matakan kamfanin PETCO, duba da yadda duniya ke fuskantar kalubalen yadda a kowace shekara ake jigbe tan miliyan 8 na robobi a cikin teku .(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China