in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya da Kamfanin Huawei za su hada hannu don bibiyar ingancin ruwa
2018-11-27 10:55:14 cri

Kasar Kenya da kamfanin fasaha na kasar Sin Huawei, na shirin hada hannu domin bibiyar ingancin ruwa da nufin bunkasa samar da tsaftataccen ruwa.

Fred Nyongesa, manajan kula da ingancin ruwa na hukumar albarkatun ruwa ta Kenya WRA, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, yayin taron tattalin arzikin albarkatun ruwa dake gudana a Nairobi cewa, suna tattaunawa game da cimma yarjejeniya da Huawei, domin fara sanya ido kan ingancin ruwa a farkon shekarar 2019.

Karkashin yarjejeniyar, kamfanin Huawei zai kafa na'urorin tattara bayanai a cikin ruwa, domin su rika aikewa da bayanan ingancin ruwa zuwa ga rumbun adana bayanai na hukumar WRA, a lokacin da suke daukar bayanan, wanda ke da nufin duba kwayoyin hallita dake haifar da cututtuka da kuma inganta tsaron halittun cikin ruwa.

Fred Nyongesa, ya ce da zarar an kafa na'urorin, za su ba gwamnati damar bibiyar masu gurbata ruwa a daidai lokacin da suke aikin, ta hanyar amfani da bayanan da za a rika samu daga wuraren.

Ya kara da cewa, yanzu a kasarsa kaso 60 na saman ruwan dake yankunan birane da kuma kaso 40 na dukkan matattarar ruwa dake yankunan karkara a gurbace suke.

Har ila yau, ya ce gurbatar matattarar ruwa na faruwa ne galibi saboda yadda ake zuba nau'ikan dauda cikin koguna da tafkuna da koramu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China