in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci kasa da kasa da su yi amfani da sabbin fasahohin kare muhalli
2019-03-10 16:35:50 cri

Babban wakilin kasar Sin mai kula da sauyin yanayi ya bukaci shugabannin kasashen duniya da su rungumi amfani da sabbin fasahohin zamani wajen ayyukan kare muhalli don cimma nasarar da aka sanya gaba na yaki da sauyin yanayi a duniya baki daya.

Xie Zhenhua, wakilin musamman na kasar Sin game da harkokin sauyin yanayi, ya bayyana cewa, muddin kasashen duniya suna burin warware matsalar da suka shafi sauyin yanayi, ya zama tilas su rungumi amfani da sabbin fasahohin zamani maimakon fasahohin gargajiya da ake amfani da su.

Kayayyakin da ake amfani da su masu tsimin makamashi, da marasa fitar da hayaki mai gurbata muhalli, da bunkasa makamashi mai tsabta, su ne matakan da suka dace a yi amfani da su, in ji Xie, inda ya bayyana hakan a lokacin taron dandalin kasa da kasa karo na biyu na MDD game da batun inganta manufofin kimiyyar kare muhalli da aka shirya a birnin Nairobin kasar Kenya.

Ya bukaci gwamnatocin kasashen duniya da su hada gwiwa da al'ummomin kasashensu, da kungiyoyi masu zaman kansu, da masana a cibiyoyin ba da ilmi, domin tabbatar da cimma nasarar kare muhalli.

Xie ya bayyana cewa, irin wadannan matakai sun yi matukar tasiri a kasar Sin, inda aka wayar da kan al'ummomin mazauna kasar game da irin rawar da za su taka wajen magance matsalolin da suka shafi sauyin yanayi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China