in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya za ta kyautata ingancin kayayyaki don shiga kasuwannin Sin
2019-01-20 15:41:48 cri

Wani masani ya ce kamata ya yi kasar Kenya ta kara kyautata ingancin kayayyakin da take samarwa domin su kara yin gogayya a kasuwannin kasar Sin.

Bitange Ndemo, wani farfesa ne a fannin tattalin arziki dake jami'ar Nairobi, ya ce yin bincike game da yanayin da kasuwannin kasar Sin ke ciki shi ne matakin farko da zai taimakawa kayayyakin da kasar Kenya ke samarwa don samun karbuwa a kasuwannin kasar Sin, kasar dake kan gaba a karfin tattalin arziki a duniya.

Ndemo ya fada cewa, idan kasar ta Kenya tana da burin samun gagarumar karbuwa a kasuwannin kasar Sin, to ya zama wajibi gwamnatin kasar ta aiwatar da wani tsarin musamman game da batun filayen noma wanda zai kara karfafa gwiwa don zuba jari a fannin aikin gona na zamani wanda za'a samu isassun kayayyaki, ta yadda kasar za ta dinga fitar da kayayyakin amfanin gonarta mai dinbin yawa zuwa ketare.

Sannan ya bukaci a bullo da wani tsari wanda zai samar da fifiko ga kayayyakin da kasashen Afrika ke fitarwa ketare.

Kenya tana muradun kara fitar da kayayyakinta zuwa kasuwanni kasar Sin, da suka hada da furanni da kayan marmari, in ji kwararran masanin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China