in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ce kaura zuwa birane za ta kara fadada a Habasha
2019-03-05 11:00:30 cri

Hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD ECA, ta ce an yi hasashen karuwar kaura zuwa birane a kasar Habasha za ta ninka sau 3, inda adadin mutane dake zaune a birane zai kai miliyan 42.3 ya zuwa shekarar 2037.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, hukumar ta ce ban da karuwar jama'a da ake sa ran samu, manyan birane za su kara cika.

Sanarwar ta ce, har yanzu kaura da ci gaban birane na matakinsu na farko a kasar, abun da zai ba da damar taimakawa samun ci gaba da taimakawa ayyukan masana'antu da cimma muradun ci gaba masu dorewa a kasar.

A cewar ECA, gwamnatin Habasha ta samar da wani ingantaccen tsarin da zai kai ta ga raya birane, sannan, ta mayar da tsarin shugabanci na gari da bunkasa kwarewarta a matsayin abubuwan da ta sanya gaba.

Cikin shekaru 10 da suka gabata, Habasha ta aiwatar da zagaye 2 na shirin shekaru 5, na manufofinta na tsarin ci gaba da gyare gyare, wadanda suka hada da muradun ci gaba masu dorewa da ake son cimmawa ya zuwa shekarar 2030. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China