in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabancin kwamitin tsaron MDD da Habasha za ta karba a Satumba zai mayar da hankali kan warware tashin hanlalin dake faruwa a Afirka
2017-08-30 13:12:07 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Habasha Meles Alem ya bayyana cewa, kasarsa za ta mayar da hankali kan matakan warware rikice-rikicen dake faruwa a nahiyar Afirka, yayin da take shirin karbar shugabancin karba-karba na kwamitin sulhun MDD na watan Satumban wannan shekara.

Mr Meles ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kasashen da Habashan za ta mayar da hankali kan su, sun hada da Somaliya, da Sudan ta kudu da kuma manyan tafkunan Afirka. Ya ce, daya daga cikin matakan da za ta dauka na warware tashe-tashen hankulan da kasashen nahiyar ke fuskanta, sun hada da kiran taron kasashe mambobin kwamitin sulhu wanda za a gudanar a birnin Addis Ababan kasar ta Habasha daga ranakun 7 zuwa 8 ga watan Satumban wannan shekara.

Ya ce, tuni kasar ta Habasha ta shirya shiga tsakani, musamman a tashin hankalin dake faruwa a kasashen Somaliya da Sudan ta kudu, ta hanyar kungiyar IGAD, wadda kasashen uku ke zama mambobinta.

Haka kuma Habashan za ta shirya wani taron koli a ranar 20 ga watan Satumba, a kokarin kara karfi da yawan dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD dake gudanar da ayyukan samar da zaman lafiya a sassa daban-daban na nahiyar. Yanzu haka dai kasar ta Habasha ce ke kan gaba wajen bayar da gudummawar dakarun wanzar da zaman lafiya a nahiyar Afirka, kana ta hudu a duniya a wannan fanni. Wannan ko ya hada da tawagogin MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya a yankin Darfur da Liberia da Sudan ta kudu, da Cote d'Ivoire da yankin Abyei dake tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta kudu, inda kasar ta Habasha ta tura dakaru 4,400 .(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China