in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Likitoci a Nijeriya za su dakile barkewar cutar zazzabin Lassa
2019-01-29 09:34:53 cri

Likitoci a Nijeriya, sun ce suna shirya yadda za su dakile barkewar cutar zazzabin Lassa a kasar.

Da yake ganawa da manema labarai jiya a Abuja, babban birnin kasar, shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasar (NARD) Olusegun Olaopa, ya ce sake bullar zazzabin a baya-bayan nan abun damuwa ne.

A cewar cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta kasar, daga ranar 1 zuwa 13 ga watan Junairun bana, jimilar mutane 172 ne ake zargin sun kamu da cutar, inda daga cikinsu aka tabbatar 35 sun kamu.

Olusegun Olaopa ya ce, kungiyarsu ta kuduri niyyar taimakawa kokarin gwamnati da jami'an kiwon lafiyar al'umma wajen karewa da tunkarar barazanar lafiyar al'umma. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China