in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 2 sun mutu bayan bullar zazzabin Lassa a babban birnin Najeriya
2018-04-19 09:20:42 cri

Mutane biyu sun mutu a Abuja, fadar mulkin tarayyar Najeriya bayan bullar cutar zazzabin Lassa wadda ta barke tun a farkon wannan shekara, ta bazu zuwa kusan jihohin kasar 20, hukumomin lafiya na yankin ne suka tabbatar da lamarin a ranar Laraba.

Wani jami'in hukumar lafiya ta yankin Humphrey Okoroukwu, ya ce mutanen da suka mutu na daga cikin wadanda suka kamu da cutar zazzabin a cikin watanni uku a birnin Abuja.

Okoroukwu, wanda ke shugabantar sashen kiwon lafiyar jama'a na Abuja, ya ce an samu rahoton bullar cutar kimanin 38 a birnin, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a kwaryar babban birnin kasar.

A kalla mutane 120 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon kamu da cutar kawo yanzu a cikin jihohin kasar 19, ciki har da babban birnin kasar Abuja, tun bayan da aka samu rahoton farko na bullar cutar a ranar 1 ga watan Janairu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China