Mai magana da yawun ma'aikatar Gao Feng, wanda ya bayyana hakan jiya Alhamis, ya ce, tsarin ya kunshi, sanya tsarin cudanyar kasashen duniya a harkokin cinikayya, kana ko wace mamban kungiyar tana da 'yancin zabar manufofi cinikayya da tattalin arzikin ketare da ya dace da ita.
Yarjeniyar kungiyar WTO ta kunshi tanade-tanaden tsarin na SDT, wanda ya baiwa kasashe masu tasowa 'yanci na musamman, misali, za su iya alkawarin cimma daidaito kan rage haraji maimakon kasashen da suka ci gaba wajen sasantawa a fannin cinikayya.
Da yake karin haske kan yadda kasashe masu tasowa suka amince su janye 'yancinsu na SDT a sasantawa a WTO, Gao, ya ce, kasar Sin, babbar kasa ce mai tasowa, kuma a shirye take ta sauke nauyin dake kanta daidai da matsayi da kuma karfin ci gabanta.
Ya ce, kasar Sin za ta hada kai da sauran kasashe masu tasowa, wajen kare 'yancinsu. Kana a nasu bangare kuma, ya kamata dukkan mambobin WTO, su martaba juna su kuma yi kokarin ganin an yiwa kungiyar gyaran fuska, bisa tsarin cudanyar kasashen duniya.(Ibrahim)