in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamaru ta yi watsi da rahoton hukumar kare hakkin dan adam game da yankin dake magana da Turanci
2019-04-04 10:47:57 cri
A ranar Talata kasar Kamaru ta ce tayi watsi da abin da ta kira "goyon bayan wani bangare" game da rahoton da hukumar dake sanya ido kan kare hakkin bil adama (HRW) dake da sansaninta a Amurka ta fitar dangane da yawan kashe kashen rayukan da ake fuskanta a yankunan kasar Kamaru masu magana da yaren Turancin Inglishi.

Hukumar ta HRW ta wallafa wani rahotonta a ranar 28 ga watan Maris, inda ta zargi dakarun tsaron kasar Kamaru da kashe fararen hula masu dunbun yawa, ta hanyar nuna karfin da ya wuce kima, da muzgunawa daruruwan mutane har suke kauracewa gidajensu sama da watanni 6 da suka gabata.

Gwamnatin Kamaru ta yi fatali da wadannan jerin zarge zarge wadanda ta ce sun ci karo da fafutukar da dakarun tsaron kasar ke yi na tabbatar tsaron dukkan yankunan kasar, ministan sadarwar na kasar kana mai magana da yawun gwamnatin kasar Kamaru, Emmanuel Rene Sadi shi ne ya bayyana a taron manema labarai.

Ministan ya zargi hukumar ta HRW da nuna rashin adalci tare da goyon bayan dakaru masu dauke da makamai. Ya ce kasar Kamaru tayi matukar mamaki ganin yadda rahoton bai ce uffan ba game da yawaitar garkuwa da mutane, da rufe makarantun kasar, da kone asibitoci da sauran kashe kashen rayukan da 'yan arewan masu dauke da makamai ke aiwatarwa a sassan kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China