Wani jami'in kungiyar Raymond Mbah ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an sace kocin ne a garin Bamenda a gefen motarsa. Ya ce suna fatan yana nan lafiya a duk inda yake. Ya kara da cewa, Emmanuel Bosso, koci ne kawai ba dan siyasa ba, don haka ba su san dalilin da ya sa aka sace shi ba.
Har ila yau, ya ce shugabancin kungiyar ya gudanar da taro domin tabbatar da kubutar da shi lami lafiya.
Emmanuel Bosso, shi ne babban jami'in kwallon kafa na farko da aka sace, tun bayan fara rikici a yankunan biyu dake da rinjayen masu amfani da harshen ingilishi a watan Nuwamban 2017. (Fa'iza Musatpha)