in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sako dalibai 20 da aka yi garkuwa da su a yankin masu magana da yaren Turanci a Kamaru
2019-03-22 16:09:12 cri

A daren ranar Alhamis aka sako daliban nan 20 'yan kungiyar wasan kwallon kafan jami'ar Buea wadanda aka yi garkuwa da su a ranar Laraba, bayan sun sha dan banzan duka a hannun masu garkuwar, hukumomin jami'ar ne suka sanar da hakan.

Dukkan daliban su 20 an sako su ne da misalin karfe 8 na dare, sai dai suna cikin mawuyacin hali. Wasu daga cikin daliban an ji musu raunuka, wasu daga cikinsu ba sa cikin hayyacinsu kuma suna tsananin bukatar kulawar likitoci ta gaggawa, in ji Nicolas Asongu, kociyan 'yan wasan, ya bayyanawa manema labarai, ya ce tuni aka garzaya da wasu daliban zuwa asibiti.

Rahotannin farko sun nuna cewa an yi garkuwa ne da dalibai 15 yayin da suke samun horo a Buea, babban birnin shiyyar kudu maso yammacin kasar, wanda ya kasance daya daga cikin yankunan da ake magana da yaren turancin Ingilishi a jamhuriyar Kamaru.

Sai dai ba'a tantance takamamman wanda ke da alhakin yin garkuwa da daliban ba, a daidai lokacin da yankunan biyu suke cigaba da fuskantar ayyukan masu garkuwa da mutane.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China