in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya gana da mataimakiyar sakataren MDD
2018-11-22 19:51:23 cri

A yau ne mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya gana da mataimakiyar babban sakataren MDD Amina Mohammed a nan birnin Beijing.

Yayin ganawar, Wang ya bayyana MDD a matsayin tambarin kasancewar bangarori daban-daban, kana cibiyar hadakar bangarori, don haka a halin da ake ciki, al'ummomin kasa da kasa na bukatar MDD mai cike da kuzari fiye da can baya.

Wang ya kara da cewa, a matsayinta na kasa mai kujerar din-din-din a kwamitin sulhun MDD, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan manufar kasancewar bangarori daban-daban yayin da MDD za ta kasance a kan gaba wajen jagorantar harkokin kasa da kasa, da kare 'yanci da muradun kasashe masu tasowa.

Haka kuma a shirye kasar Sin ta ke wajen yin aiki tare da MDD game da batutuwan kasa da kasa, ciki har da tunkarar matsalar sauyin yanayi da hada kai wajen kulla alaka karkashin shawarar ziri daya da hanya daya.

A nata jawabin, Amina Mohammed ta yaba da yadda kasar Sin ke goyon bayan kasancewar bangarori daban-daban da ma ayyukan da MDD take gudanarwa. Kana MDD za ta ci gaba da hada kai tare da kasar Sin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China