in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin: Sin za ta ci gaba da shiga aikin kiyaye zaman lafiya na MDD
2019-02-13 19:47:36 cri

Yau Laraba kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing cewa, a matsayinta na muhimmiyar kasa wadda take tura sojojin kiyaye zaman lafiyarta zuwa kasashen dake bukata haka kuma take biyan kudin karo karo ga MDD a kan lokaci, kasar Sin tana taka babbar rawa wajen maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wasu kasashe da yankunan da abin ya shafa, a sa'i daya kuma tana kokarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi na al'ummomin wuraren, ana iya cewa, tana sauke hakkin dake wuyanta yadda ya kamata.

Kwanan baya aka kaddamar da bikin nune-nune game da babban taken "sojojin kasar Sin wadanda ke kiyaye zaman lafiya a fadin duniya" a hedkwatar MDD dake birnin New York na kasar Amurka, mataimakin babban sakataren MDD Atul Khare shi ma ya halarci bikin, inda ya bayyana cewa, kasar Sin tana ba da muhimmiyar gudumowa a aikin kiyaye zaman lafiya na MDD. Madam Hua Chunying ita ma ta yi nuni da cewa, gwamnatin kasar Sin ta yabawa sharhin da mataimakin babban sakataren MDD Atul Khare ya yi kan kokarin da kasar Sin take a fannin kiyaye zaman lafiya a fadin duniya.

Hua ta nuna cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nuna kwazo da himma domin kara goyon bayan aikin kiyaye zaman lafiya na MDD, haka kuma tana son hada kai tare da sauran kasashen duniya domin aiwatar da ka'idojin MDD, tare kuma da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin duniya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China