in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mamban majalisar gudanarwar Sin ya gana da wakilan kasashe mambobin kwamitin sulhun MDD
2018-11-27 09:32:55 cri

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya gana a jiya da wakilan din din din na kasashe mambobin kwamitin sulhu na MDD dake ziyara a kasar Sin.

Da yake bayyana MDD a matsayin alama ta dangantakar kasa da kasa, Wang Yi ya jadadda cewa, ya kamata dukkan bangarori su yi biyayya ga dokokin kasa da kasa, irinsu ka'idoji da manufofin MDD, domin ci gaba da inganta dangantakar kasa da kasa cikin kyakkyawan yanayi.

Ya ce, al'ummomin kasa da kasa na bukatar MDD ta taka rawar gani, sannan ya kamata kwamitin sulhu dake da alhakin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali, ya kare hulda da dokokin kasa da kasa.

A nasu bangaren, wakilan sun yabawa kasar Sin bisa yadda take kiyaye dangantakar kasa da kasa da goyon bayan da take ba MDD da gagarumar gudunmuwar da take ba ayyukan wanzar da zaman lafiya na majalisar da inganta ci gaban duniya. Sun kuma ce a shirye suke su yi aiki da kasar Sin wajen kiyaye tsaro da zaman lafiya a duniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China