in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Aljeriya ya sauka daga mukaminsa
2019-04-03 19:11:20 cri

A jiya Talata ne, shugaba Abdelaziz Bouteflika na kasar Aljeriya, ya sanar da yin murabus daga mukaminsa, makwanni uku kafin karewar wa'adin mulkinsa a ranar 28 ga watan Afrilu.

Kamfanin dillancin labarai na APS ya ruwaito cewa, majalisar kundin tsarin mulkin kasar, na shirin kiran taron gaggawa don amincewa da murabus din shugaban kafin ta sanar a hukumance.

Shugaba Bouteflika wanda aka fara zaba a mukamin shugabancin kasar a shekarar 1999, an sake zabarsa a wa'adi na hudu a shekarar 2014, inda ya yi mulki kasar na wasu shekaru biyar. Dubban jama'a ne dai suka bazama kan tituna a sassan kasar, lokacin da shugaban ya sanar sa aniyarsa ta sake neman wa'adi na biyar a watan Fabrairu, suna bukatarsa da ya janye wannan shawara ta neman sake tsayawa takara.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China