in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin Aljeriya ta gano makamai da dama a kusa da iyakar kasar da Mali
2018-08-04 15:44:48 cri

Ma'aikatar tsaron Aljeriya, ta ce sojoji sun gano makamai masu tarin yawa a kusa da iyakar kasar da Mali.

Ma'aikatar ta ce, sojojin sun gano bindiga mai sarrafa kansa kirar Kalashnikov da wasu nau'ika daban-daban na bidigogi, da alburasai da kuma dama, a wani ginin karkashin kasa dake yankin Bordj Badji Mokhtar dake kudancin kasar.

Har ila yau a wani ginin na karkashin kasa a yankin, an kuma gano wasu bindigogi masu sarrafa kansu na Kalashnikov da wasu nau'ikan bindigogi da rokoki 11 da tarin ababen fashewa da alburusai.

A daya bangaren kuma, wasu tsageru biyu sun ajiye makamansu, inda suka mika wuya ga sojojin dake lardin Tamanrasset na kudancin kasar, wanda ke kan iyaka da Mali da Niger.

Sanarwar da ma'aikatar tsaron ta fitar, ta ce wadannan ayyuka sun nuna yadda ake sa ido sosai da kuma kudurin sojoji na dakile duk wani yunkuri na yin nakasu ga tsaro da zaman lafiya a kasar.

Gwamnatin Aljeriya, ta tura dubban dakarun zuwa iyakokinta na kudu da gabas, a wani yunkuri na dakile kutsen 'yan ta'adda da makamai, yayin da ake tsaka da fama da rashin tsaro a Mali da kuma yakin basasa a Libya.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China