in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aljeriya ta yi kira da a toshe kafofin da 'yan ta'adda ke samun kudade
2018-11-28 10:10:38 cri

Ministan harkokin wajen Aljeriya Abdelkader Messahel ya bayyana cewa, har yanzu kasashen duniya sun gaza toshe kafofin da kungiyoyin 'yan ta'adda ke samun kudadensu.

Messahel ya bayyana hakan ne yayin taron rukunin yammacin Afirka game da yaki da ayyukan ta'addanci a duniya karo na biyu wanda ya gudana a birnin Algiers. Ya kuma bukaci kasashen duniya da su kara hada kai don ganin an toshe duk wasu hanyoyi da kungiyoyin 'yan ta'adda ke samun kudaden nasu.

Ministan ya ce, 'yan ta'addan suna samun makuden kudaden ne daga safarar miyagun kwayoyi da makamai ta hanyar munanan laifuffukan da suke aikatawa a kan iyakokin kasashe. Suna kuma amfani da wadannan kudade wajen daukar sabbin magoya baya.

Taron ya samu halartar masana sama da 100 a fannonin kandagarki da yaki da ta'addanci gami da tsattsauran ra'ayi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China