in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Aljeriya zai shiga takarar neman mulkin kasar
2019-02-11 14:12:59 cri

Shugaban kasar Aljeriya, Abdelaziz Bouteflika ya sanar da kudurinsa na shiga babban zaben shugaban kasar da za a shirya a ranar 18 ga watan Aflilun dake tafe.

Shugaba Bouteflika ya bayyana haka ne a jiya, cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya bayyana cewa, idan ya lashe zaben, zai kafa wani kwamiti da zai yi gyaran fuska kan siyasa da tattalin arziki da zaman takewar al'umma a fadin kasar tun daga shekarar bana da muke ciki.

Abdelaziz Bouteflika yana da shekaru 81 yanzu, ya fara mulkinsa a kasar Aljeriya ne a shekarar 1999, daga baya kuma ya rika lashe babban zaben kasar har sau uku wato a shekarar 2004 da 2009 da kuma 2014.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China