in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a kaddamar da bikin fina-finan kasa da kasa na Beijing karo na 9
2019-04-03 19:01:32 cri

Za a kaddamar da bikin fina-finan kasa da kasa na birnin Beijing karo na 9 a ranar 13 ga wata, inda za a ba da lambar yabo ta Tiantan. Yau Laraba 3 ga wata, hukumar shirya bikin ta sanar da cewa, gaba daya fina-finai 15 wadanda suke kunshi "The Wandering Earth" da "The Eleventh Chapter" za su shiga takarar neman samun lambar yabon.

An kafa lambar yabon "Tiantan" ne a shekarar 2013, har kullum ana nacewa ga tunanin martaba juna kan bambancin al'adu yayin da ake zabar fitattun fina-finai a fadin duniya, a sa'i daya kuma, ana kokari matuka domin bunkasa cudanyar fina-finai dake tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a ciyar da fasahar fina-finai gaba yadda ya kamata.

Bayanai na cewa, alkalan gasar sun hada da shahararrun masana da abin ya shafa a fadin duniya guda 7, wadanda suka kunshi shahararren darektan fina-finai na Amurka Rob Minkoff. Mataimakiyar babban sakataren hukumar shirya bikin Xing Bo ta yi bayani cewa, dukkan alkalan gasar sun kware matuka a bangaren, kuma sun taba shirya fina-finan da suka samu karbuwa sosai a wajen 'yan kallo, sun kuma taba samun lambobin yabo iri daban daban a bukukuwa iri daban daban a fadin duniya.

Za a rufe bikin ne a ranar 20 ga wata.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China