in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da "bikin nunin fina-finan kasar Sin a Afirka" a Afirka ta Kudu
2018-07-18 21:41:28 cri

Yau Laraba ne, a birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu, aka kaddamar da "bikin nunin fina-finan kasar Sin a Afirka", wanda ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, gami da babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice suka shirya cikin hadin-gwiwa.

Mataimakin shugaban hukumar yayata bayanai ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, gami da sauran wasu manyan jami'ai daga kasashen Afirka ta Kudu da Botswana sun halarci bikin.

A nata bangaren, shugabar karba-karba ta kwamitin kula da harkokin kudi na gamayyar kasashen kudancin Afirka ko kuma SADC a takaice, Nthabiseng Khunou ta yi jawabi, inda ta ce, bikin nunin fina-finan kasar Sin a Afirka, zai kara samar da fahimtar juna tsakanin jama'ar Sin da Afirka, kuma tana maraba da zuwa fina-finan kasar Sin a nahiyar ta Afirka. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China