Bugu da kari, sassan biyu sun yi musayar ra'ayoyi kan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya dake shafarsu. Sun kuma kalli yadda aka sanya hannu kan muhimman takardun hadin gwiwa kan haraji da aikin gona da harkokin kudi da binciken kimiyya. Daga bisani kuma su ka fitar da sanarwa kan matsalar sauyin yanayi.
A jiya Lahadi ne dai, Ardern ta iso birnn Beijing, fadar mulkin kasar Sin, kuma wannan shi ne ziyarar aikinta ta farko a kasar Sin, tun bayan da ta zama sabuwar firaministar kasar New Zealand.(Ibrahim)