in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: ya wajaba a rika martaba dokokin kasa da kasa na jin kai
2019-04-02 10:19:41 cri
Sakataren ofishin MDD mai lura da ayyukan jin kai Mark Lowcock, ya shaidawa taron kwamitin tsaron majalissar, bukatar dake akwai game da kara kaimi wajen kare fararen hula, da martaba matakan jin kai.

Lowcock ya bayyana hakan ne, yayin wani zaman muhawara da ya gudana a jiya Litinin, yana mai cewa an kafa dokokin jin kai na kasa da kasa ne, domin su dakile wahalhalu da al'ummu ke fuskanta a lokutan yake-yake, su kuma ba da damar samar da agajin jin kai a duk lokacin da ake bukatar su.

Jami'in ya ce a bana, mutane da yawansu ya kai miliyan 139 na bukatar tallafin jin kai, mafi yawansu sakamakon tashe-tashen hankula masu nasaba da masu dauke da makamai.

Ya ce adadin ya ninka sau 3, sama da na shekaru 10 da suka gabata. Kaza lika kaso kusan 60 bisa dari na mutanen dake fuskantar matsalar karancin abinci a duniya, na zaune ne a kasashe dake fama da rikice-rikice. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China