in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta baiwa sauran kasashen duniya muhimman bayanai kan yanayi daga taurarinta na dan Adam
2017-10-25 10:01:55 cri

Babban darektan cibiyar harkokin tauraron dan Adam mai kula da harkar yanayi na kasar Sin Yang Jun ya bayyana kudurin kasarsa na baiwa ragowar kasashen duniya muhimman bayanai game da yanayi da sabbin taurarin dan Adam dinta na Fengyun-4 da Tansat suka tattara.

Yang Jun wanda ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a ranar kasar Sin na makon nazarin muhalli na duniya na wannan shekara da ya gudana a birnin Washington,D.C na kasar Amurka, ya ce, wadannan taurarin dan-Adam guda biyu su ne za su rika bayar da sabbin sakamako kan kirkire-kirkiren kimiyya da fasahar kere-kere a kasar ta Sin, da irin gudummawar da kasar Sin take bayarwa a duniya a fannin riga kafin aukuwar bala'u daga indallahi, tunkarar matsalar sauyin yanayi, da ci gaban tattalin arzikin da zamantakewar al'umma.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China