in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron na'urorin masu sarrafa kansa na duniya karo na biyu a Geneva
2018-05-16 10:25:24 cri

A jiya Talata ne aka bude taron kolin na'urorin masu sarrafa kansa na duniya karo na biyu a birnin Geneva, taron da ke fatan kirkiro ayyukan da na'urori masu sarrafa kansu za su taimaka ga cimma nasarar manufofin muradun karni (SDGs), kamar yadda shugaban kungiyar harkokin sadarwa na kasa da kasa (ITU) ya sanar yayin jawabinsa na bude taro.

Shi ma babban sakataren kungiyar ta ITU Zhao Houlin ya bayyana yayin bude taron kolin kungiyar a shekarar da ta gabata cewa, akwai bukatar kasashen duniya su rika tattauna yadda al'umma za ta ci gajiyar wadannan na'urori. Wannan ya sa taron na wannan karo zai mayar da hankali kan matakai da muhimman ayyukan da ake fatan aiwatarwa.

Taron na kwanaki uku wanda kungiyar ITU ta shirya, ya tattara masana daga sassa daban-daban da kwararru daga gwamnatoci, da masana'antu da jami'o'i da kungiyoyin fararen hula, wadanda za su jagoranci tawagogi hudu da za su kaddamar da ayyukan da ake fatan aiwatarwa cikin watanni masu zuwa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China