in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara zaben shugaban kasar Ukraine
2019-03-31 17:08:24 cri
Da sanyin safiyar ranar Lahadi aka bude rumfunan zabe don zabar shugaban kasar Ukraine inda 'yan takara 39 zasu fafata don neman darewar kujerar shugabancin kasar

Babbar hukumar shirya zaben kasar Ukraine (CEC) ta yiwa masu sanya ido 'yan kasashen waje kimanin 2,344 rajista wadanda suka fito daga kasashen duniya 16 da kungiyoyin kasa da kasa 15 domin su sanya ido a zaben da za'a gudanar.

A bisa ra'ayoyi daban daban da aka bayyana, shugaban kasar mai ci Petro Poroshenko, da 'yan takarar jam'iyyun hamayya Yulia Tymoshenko da mai wasan kwaikwayo Volodymyr Zelensky su ne ke sahun gaba cikin 'yan takarar.

Idan ba'a samu mutum guda cikin 'yan takarar 39 da ya samu sama da kaso 50 na kuri'un da za'a kada a zagayen farko ba, 'yan takara biyu da suka fi yawan kuri'u ne zasu fafata a zagaye na biyu na zaben wanda zai gudana a ranar 21 ga watan Afrilu. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China