in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin Sulhu na MDD ya yi kira da a samar da kayayyakin agaji ga yankunan dake hannun 'yan tawaye a Ukraine
2019-02-13 10:57:50 cri

Kasashen Tarayyar Turai dake kwamitin sulhu na MDD, sun bukaci a samar da kayayyakin agajin jin kai ga yankunan dake hannun 'yan aware a gabashin Ukraine.

Bayan shafe shekaru 5 ana rikici, tabarbarewar yanayin tsaro a gabashin Ukraine na kara tasiri kan fararen hula, musammam wadanda ke zaune a wuraren da ba sa karkashin ikon gwamnati, baya ga barazanar da suke fuskanta na hare-hare.

Wata sanarwa da kasashen suka fitar ta bukaci dukkan bangarori dake rikici, su sake samar da damar da kungiyoyin agaji na kasa da kasa za su iya isa yankunan da ba sa karkashin ikon gwamnati, tare da bada damar kai agaji cikin sauri kamar yadda ka'idoji da dokokin jin kai na kasa da kasa suka tanada.

Kasashen na Tarayyar Turai, sun kuma bukaci a samar da mafita ga rikicin cikin kwanciyar hankali. Suna masu cewa sun gamsu, za a iya warware rikicin cikin lumana, a don haka suka yi kira ga dukkan bangarorin da su gaggauta aiwatar da kunshin yarjejeniyar Minsk tare da girmama kudurinsu domin cimma samun maslaha mai dorewa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China