in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta budewa jiragen ruwan Ukrain wuta a kusa da zirin Kerch
2018-11-26 10:59:38 cri
Rundunar sojin ruwan Ukraine ta ce dakarun Rasha sun budewa jiragen ruwanta wuta a kusa da zirin Kerch, lamarin da ya raunata mutum guda.

Sanarwar da rundunar ta Ukraine ta wallafa a shafin Facebook a jiya, ta ce harin ya lalata jirgin yakin kasar na Berdyansk.

Da farko a jiyan, sashen lura da kan iyaka na hukumar tsaron Rasha dake Crimea, ya ce jiragen ruwan Ukraine 3 sun take dokokin iyakar Rasha a Bakin teku na Bahr Asuwad, inda suka yi atisaye mai hadari tare da yin biris da umarnin Rashar.

Sai dai, rundunar sojin ruwan Ukraine, ta ce ta sanar da Rasha tun kafin lokacin game da wucewar jiragen daga Bakin teku zuwa tekun Azov ta zirin Kerch da ya raba tekunan biyu.

A cewar rahotannin kafafen yada labarai na yankin, Rasha ta hana jiragen ruwan Ukraine shiga tekun Azov.

Ministan harkokin wajen Ukraine ya zargi Rasha da daukar matakan takala, yana mai cewa ta take 'yancin zirga-zirga ta hanyar amfani da karfin da ba ya bisa doka a kan jiragen ruwan kasarsa.

Rasha dai ta ce binciken jirgen na da nufin tabbatar da tsaro a tekun Azov da zirin Kerch, kuma bai take dokokin kasa da kasa ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China