in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masani: Shawarar ziri daya da hanya daya ta taimaika ga ci gaban Afirka
2019-03-04 19:46:48 cri

Darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin dake Najeriya Charles Onunaiju ya ce, shawarar ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta gabatar da nufin bunkasa alakar kasa da kasa, za ta taimakawa nahiyar Afirka, nahiya ta biyu mafi girma, kana ta biyu mafi yawan al'umma a duniya.

Darektan wanda ya bayyana hakan yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Abuja, fadar mulkin Najeriya, ya ce shawarar ta samarwa nahiyar Afirka da dukkan damammakin bunkasuwa da ake bukata.

Onunaija ya ce, lokacin da kasashen nahiyar suka fara samun 'yancin kai shekaru 60 da suka gabata, abin da masu kishin nahiyar suka sanya a gaba, na farko shi ne kokarin gina nahiyar ta yadda za ta tsaya da kafunta, saukaka harkokin cinikayya tsakanin al'ummomin nahiyar da sauran su

Sai dai kuma jami'in ya ce, duk wadannan mafarki ba su gaskata ba, saboda matsaloli a fannonin yanayi da hadewar hukumomi. Amma ya ce yanzu shawarar ziri daya da hanya daya ta samar da damammakin da nahiyar ke bukata wajen cimma burin da ta sanya a gaba. Ya kara da cewa, shawarar ta kuma taimaka wajen hade shiyyar ta yadda jama'a za su iya yin cudanya da juna cikin sauki.

Bugu da kari, shawarar ziri daya da hanya daya, ta cike gibi na tarihi da ya dade tun kafin samun 'yancin kan nahiyar. Kana shawarar ta kasance mai muhimmanci ga nahiyar da ma ci gabanta.

Haka kuma, nahiyar Afirka tana da wata dama ta musamman da za ta iya amfani da shawarar wajen shiga tsarin kasa da kasa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China